Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

Ra'ayoyin masu saurare kan shirin maja tsakanin Atiku da Obi a zaɓen 2027

Informações:

Sinopsis

Tsohon mataimakain shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023 da ya gabata Atiku Abubakar da kuma ɗan takarar LP a 2023 Peter Obi na shirin haɗewa domin kawar da gwamnatin APC wadda a cewarsu ta gaza, lamarin da ke zuwa tun kafin kakar zaɓen na shekarar 2027. Sai dai a martaninta, jam’iyyar APC ta ce babu wata haɗaka da za ta iya taka wa shugaba mai ci birki.Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...