Bakonmu A Yau

Alhaji Muhammadu Magaji kan kuɗin da aka warewa fannin noma a kasafin kuɗin Najeriya

Informações:

Sinopsis

Kasafin kuɗin Najeriya na cigaba da zama abin muhawara tun bayan da shugaba Bola Tinubu ya gabatar da shi a gaban ƴan Majalisun Dokokin ƙasar a makon jiya. Baya ga kason da aka ware don biyan bashi, da tsaro, da sauran fannoni, kuɗaɗen da aka warewa noma na daga cikin batutuwan da suka fi ɗaukar hankali, la’akari da cewar duk da muhimmancinsa, fannin ya gaza samun kashi biyu ko sama da haka, daga cikin kasafin na shekara mai zuwa da ya haura naira Tiriliyan 47. Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da Alhaji Muhammadu Magaji Sakataren tsare tsare na Ƙungiyar Manoman Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar tattaunawarsu........