Bakonmu A Yau

Michael Wetkaz kan kamen ƴan damfara ƴan ƙasashen waje 792 da EFCC ta yi a Lagos

Informações:

Sinopsis

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya EFCC ta kama ƴan damfara 792 da suka haɗa da Larabawa da ƴan China da Philippines a birnin Lagos, kamen da shi ne mafi girma da hukumar ta yi a rana guda kuma a lokaci guda. Darektan Hulɗa da Jama'a na EFCC Wilson Uwajaren ya ce, waɗannan mutanen sun shahara wajen damfara ta yanar gizo, inda suke ɓoye kamanninsu tare da gabatar da soyayya ta ƙarya domin yaudarar jama'a a sassan duniya.  Ku latsa alamar sauti don jin tattaunawar Abdurrahman Gambo Ahmad da mukaddashin darektan EFCC a Lagos, Mr. Michael Wetkaz.....