Bakonmu A Yau
Dr. Abdulhakim Garba Funtua: Makomar Syria a ƙarƙashin sabuwar gwamnati
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editor: Podcast
- Duración: 0:03:40
- Mas informaciones
Informações:
Sinopsis
Majalisar Ɗinkin Duniya ta shiga sahun ɓangarorin da suka fara nuna goyon baya ga sabuwar gwamnatin Syria, a wani yanayi da shugaba Abu Mohammad al-Julani da Firaminista Mohammed al-Bashir suka faro shugabancin riƙon kwarya gadan-gadan, kodayake kiraye-kiraye na ci gaba da tsananta don ganin jagororin sun yi taka-tsan-tsan a salon mulkinsu don kaucewa sake faɗawar ƙasar a yaƙi. Dangane da wannan Azima Bashir Aminu ta tuntuɓi masanain alaƙar ƙasashen ƙetare Abdulhakeem Garba Funtua, don jin ko wannan gwamnati za ta samu cikakken goyon bayan yammacin duniya.Ku latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawarsu