Sinopsis
Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan alamurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi alumma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.
Episodios
-
Majalisar Najeriya ta gayyaci Buhari don yi mata bayani kan tsaro
08/05/2019 Duración: 10minShirin Dandalin Siyasa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya yi nazari kan kiran da Majalisar Tarayyar Najeriya ta yi shugaba Muhammadu Buhari don yi mata bayani kan tabarbarewar tsaro a kasar.
-
Rikicin shugabancin Majalisar Wakilai a Najeriya
17/04/2019 Duración: 10minShirin dandalin siyasa a wannan makon ya sake yin duba kan dambarwar neman shugabancin Majalisar Najeriyar karo na 9 da sabbin zababbun 'yan Majalisar wakilan kasar ke tafkawa. A yi sauraro lafiya.
-
Dambarwar Jam'iyyar APC kan shugabancin Majalisun Najeriya
10/04/2019 Duración: 11minHar yanzu Jam'iyyar APC ta gaza shawo kan matsalolinta da suka shafi 'yan majalisun da za su jagoranci majalisar Dattijai da ta wakilai, dai dai lokacin da ake ci gaba da fuskantar rarrabuwar kai.
-
Fatan yan Najeriya dangane da sabuwar Majalisa bayan zabe
03/04/2019 Duración: 10minBayan wata daya da kawo karshen zaben Shugaban kasa da na wasu yan majalisu a Najeriya,hankulan yan kasar da dama ya koma zuwa zauren Majalisa .Haka zalika wasu daga cikin yan majalisun da suka samu goyan bayan jama'a sun sheidawa Bashir Ibrahin Idris a cikin shirin Siyasa fatan su da kuma irinn rawar da za su iya takawa a Majalisa don kawo sauyi a siyasar kasar,banda haka wasu sun bayyana damuwa a kai.
-
Dambarwar zabukan Najeriya na 2019
20/03/2019 Duración: 10minShirin Dandalin Siyasa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne kan dambarwar zabukan Najeriya, in da Jam'iyyar adawa ta PDP ta garzaya kotu domin kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari na APC a zaben 2019, yayinda ita ma APC a jihar Bauchi ta ruga zuwa kotu duk dai akan batun na zabe.
-
Nazari kan zaben Gwamnoni a Najeriya
07/03/2019 Duración: 09minShirin Dandalin Siyasa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya yi nazari ne game da zabukan Gwamnoni na 'yan majalisun jihohin Najeriya da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa, in da ake fargabar cewa, da dama daga cikin Gwamnoni masu ci ba za su koma kan kujerunsu ba saboda wasu dalilai na siyasa.
-
Shugaba Buhari ya lashe zaben Najeriya wa'adi na biyu
28/02/2019 Duración: 11minShirin Dandalin Siyasa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne game da nasarar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya samu ta sake lashe kujerar shugabancin kasar wa'adi na biyu bayan doke babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar. Tuni Jam'iyyar PDP ta bayyana sakamakon zaben a matsayin mara inganci tana mai zargin tafka magudi a zaben,yayinda ta ce, za ta shigar da kara a kotu.
-
2019: Hankulan kasashen duniya sun karkata zuwa zabukan Najeriya
13/02/2019 Duración: 10minShirin Dandalin Siyasa na wannan mako da Bashir Ibrahim Idris ya gabatar, yayi nazari kan halin da siyasar Najeriya ke ciki, yayinda ya rage kwanaki kalilan a gudanar da zabukan kasar na 2019 a matakai daban daban. Sai kuma tsokaci da shirin ya yi kan yadda hankulan kasashen duniya ya karkata zuwa kan zabukan Najeriyar.
-
Yadda Siyasa ke gudana a Jihar Kano gabanin zaben shugaban kasa
08/02/2019 Duración: 10minShirin Dandalin Siyasa na wannan makon, ya leka jihar Kano da ke tarayyar Najeriya, ida yayi nazari kan yadda al'amuran Siyasa ke gudana, yayinda ake gaf kada kuri'a a zaben shugabancin kasar na 2019 a ranar 16 ga watan Fabarairu.
-
Dambarwar siyasar dakatar da Onnoghen
31/01/2019 Duración: 10minShirin Dandalin Siyasa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne kan dambarwar siyasar da ta kunno kai a Najeriya bayan shugaban kasar Muhammadu Buhari ya dakatar da alkalin alkalai, Walter Onnoghen bisa zargin sa da bayar da bayanan karya kan kudaden da ya mallaka.
-
Shiri kan dakatar da Babban mai shari'ar Najeriya
30/01/2019 Duración: 10minShirin Dandalin siyasa na wannan mako ya mayar da hankaline kan dakatar da babban mai shari'ar Najeriya Walter Onnonghen da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi.
-
'Yan siyasa na sauya sheka a Najeriya
17/01/2019 Duración: 10minShirin Dandalin Siyasa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne kan yadda 'yan siyasa ke ci gaba da sauya sheka a Najeriya a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben gama-gari a cikin watan gobe.
-
Kun san abin da Buhari ya fada a Akwa Ibom?
06/01/2019 Duración: 10minShugaban Najeriya Muhammdu Buhari da ya kaddamar da yakin neman zabensa a jihar Akwa Ibom, ya bayyana nasarorin da ya samu tun bayan darewarsa kan karagar mulki a shekarar 2015, in da yake cewa, gwamnatinsa ta murkushe mayakan Boko Haram duk da cewa kungiyar kan kaddamar da hare-hare jifa-jifa a yankin arewa maso gabashin kasar. Shugaban ya kuma bayyana irin nasarar da ya samu a fannin yaki da cin hanci da rashawa. Kuna iya latsa kan hoton don sauraren cikakken shirin kan yakin neman zaben Buhari a Akwa Ibom.
-
Taron sulhunta yan siyasar Najeriya daga Tsohon Shugaban kasar
12/12/2018 Duración: 10minA wani taro da Tsohon Shugaban Najeriya Abdusalami Abubakar ya shirya,taron da ya hada yan siyasa da suka hada da Muhammadu Buhari shugaban kasar,wanda kuma ya sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin sa da sauran masu karawa da shi a zaben shekara mai zuwa.Wasu na bayyana cewa ba a gayyaci dan takara Atiku Abubakar a wannan taro,cikin shirin dandalin siyasa Bashir Ibrahim Idris ya samu tattaunawa da yan Najeriya.
-
Takaddama ta kaure a wasu jam'iyyun siyasar Najeriya
28/11/2018 Duración: 10minA cikin shirin dandalin Siyasa, Bashir Ibrahim Idris ya mayar da hankali zuwa takaddama da ta kaure a yankin arewa maso gabacin Najeriya.Datijen wannan yankin sun bukaci a goyawa daya daga cikin yan takara a zaben Shugabancin kasar baya,labarin da wasu suka musanta.Bashir Ibrahim Idris ya samu zantawa da wasu daga cikin datijen yankin a cikin shirin Dandalin siyasa daga nan Rfi.
-
Rashin kasancewar mata a fagen siyasar Najeriya
14/11/2018 Duración: 10minA cikin shirin dandalin siyasa,Bashir Ibrahim Idris ya samu tattaunawa da wasu mata dangane da rashin samun mata a fagen siyasar Najeriya,wasu daga cikin yan kasar mata musaman sun bayyana aniyar su ta kasancewa daga cikin yan takara a zaben shekarar 2019.
-
Tasirin Na'urar Tantance Kuri'u a zaben Najeriya
08/11/2018 Duración: 10minSashen Hausa na RFI na farin cikin gabatar muku da sabon shirin Dandalin Siyasa da zai rika nazari game da al'amuran da suka shafi siyasar Najeriya, Nijar, Afrika da sauran kasashen duniya. Shirin na makon farko tare da Bashir Ibrahim Idris ya yi nazari ne game da tasirin na'urar tantance masu kada kuri'u a zaben Najeriya, abin da masana ke cewa, ta na taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalar magudi.
-
Dalilin yin watsi da jekadun Buhari a Majalisar Dattijai
19/11/2016 Duración: 20minShirin Dandalin Siyasa ya tattauna game da batun yin watsi da amincewa da jekadu 46 da Majalisar Dattiajan Najeirya ta yi da rikicin shugabannin Jamiyyar PDP mai adawa a Najeriya da ta dare gida biyu inda wasu ‘yan jam’iyyar ke neman a raba-gari wasu kuma ke bukatar sake lale.
-
Sharhi akan nasarar Trump
14/11/2016 Duración: 20minShirin Dandalin Siyasa ya tattauna game sakamakon zaben Amurka inda masana suka yi sharhi akan nasarar da Donald Trump dan takarar Republican ya samu bayan ya doke abokiyar takararsa Hillary Clinton ta Democrat.
-
Manufofin Clinton da Trump a zaben Amurka
08/11/2016 Duración: 20minShirin Dandalin Siyasa ya yi nazari ne game da 'Yan takarar shugabancin Amurka guda biyu Donald Trump na Republican da Hillary Clinton da Democrat tare da tattauna manufofinsu. Sannan shirin ya yi tsokaci akan tasirin zaben Amurka ga Afrika.