Sinopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodios
-
Joseph Nahum kan bubuwan ranar Kirismeti a sassan duniya
25/12/2024 Duración: 03minMabiya addinin Kirista na cigaba da bukukuwan zagayowar ranar Kirsimeti a sassan duniya don tunawa da ranar haihuwar Yesu Al Masihu da aka yi a Bethlehem da ke kudu da birnin Qudus. Sama da shekaru dubu biyu ke nan mabiya addinin Kirista suka kwashe suna gudanar da wannan biki a duk fadin duniya, ta hanyar nuna farin ciki da ƙauma da tausayin juna da sadaukarwa da dai sauransu.Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Reverend Joseph Nahum, dake garin Maiduguri, wanda ya fara da yin tsokaci kan muhimmancin ranar ta Kirsimeti.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
Amb Abubakar Cika kan mataki AES na zaman rundunonin sojinsu cikin shirin ko ta kwana
24/12/2024 Duración: 03minƘasashen AES da suka haɗa da Nijar, Mali da kuma Burkina Faso sun yi watsi da ƙarin wa’adin watanni shidda da ECOWAS ta yi musu a makon jiya, kan lokacin ficewarsu daga cikin ƙungiyar a hukumance, rangwamen da zai fara aiki a watan Janairun dake tafe. Cikin sanarwar da suka fitar, ƙasashen uku sun sanar da baiwa rundunonin sojinsu umarnin zama cikin shirin kar ta kwana. Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Ambassada Abubakar Cika tsohon Jakadan Najeriya a ƙasar Iran. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawarsu..................
-
Alhaji Muhammadu Magaji kan kuɗin da aka warewa fannin noma a kasafin kuɗin Najeriya
23/12/2024 Duración: 03minKasafin kuɗin Najeriya na cigaba da zama abin muhawara tun bayan da shugaba Bola Tinubu ya gabatar da shi a gaban ƴan Majalisun Dokokin ƙasar a makon jiya. Baya ga kason da aka ware don biyan bashi, da tsaro, da sauran fannoni, kuɗaɗen da aka warewa noma na daga cikin batutuwan da suka fi ɗaukar hankali, la’akari da cewar duk da muhimmancinsa, fannin ya gaza samun kashi biyu ko sama da haka, daga cikin kasafin na shekara mai zuwa da ya haura naira Tiriliyan 47. Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da Alhaji Muhammadu Magaji Sakataren tsare tsare na Ƙungiyar Manoman Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar tattaunawarsu........
-
Hukumomin Najeriya sun ce sama da Naira triliyan 2 aka karɓa a matsayin kuɗin fansa
19/12/2024 Duración: 03minHukumomin Najeriya sun ce mutane sama da dubu 600 'yan ta'adda masu garkuwa da mutane suka kashe daga cikin mutane sama da miliyan 2 da dubu 200 da suka yi garkuwa da su, yayin da kuma aka biya kuɗin fansa r da ya kai sama da naira triliyan 2 da biliyan 200. Dangane da wannan rahoto mai tada hankali, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin harkar tsaro Malam Yahuza Getso, kuma ga yadda zantawar tasu ta kasance.sai a latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawar.
-
Hajiya Hannatu Musawa kan sanya bikin hawan Daba na Kano cikin manyan al'adun duniya
18/12/2024 Duración: 03minHukumar da ke kula da al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta UNESCO ta damƙawa Najeriya takaddar shaidar sanya bikin hawan Daba na Kano cikin manyan al'adun duniya masu matukar tasiri. Jim kaɗan bayan kammala miƙa shaidar wakilinmu a Abuja Isma’il Karatu Abdullahi ya tattanna da ministar al’adu ta Najeriya Hajiya Hannatu Musawa kan tasirin da wannan zai yi wa ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawar ta su......
-
Michael Wetkaz kan kamen ƴan damfara ƴan ƙasashen waje 792 da EFCC ta yi a Lagos
17/12/2024 Duración: 03minHukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya EFCC ta kama ƴan damfara 792 da suka haɗa da Larabawa da ƴan China da Philippines a birnin Lagos, kamen da shi ne mafi girma da hukumar ta yi a rana guda kuma a lokaci guda. Darektan Hulɗa da Jama'a na EFCC Wilson Uwajaren ya ce, waɗannan mutanen sun shahara wajen damfara ta yanar gizo, inda suke ɓoye kamanninsu tare da gabatar da soyayya ta ƙarya domin yaudarar jama'a a sassan duniya. Ku latsa alamar sauti don jin tattaunawar Abdurrahman Gambo Ahmad da mukaddashin darektan EFCC a Lagos, Mr. Michael Wetkaz.....
-
Dr Isa Abdullahi kan ƙarancin takardun kuɗin naira a Najeriya
16/12/2024 Duración: 03minƳan Najeriya na ci gaba da bayyana damuwa a kan rashin isassun takardun kuɗaɗe a daidai lokacin da Babban Bankin ƙasar ke cewa akwai sama da naira triliyan 4 a hannun jama'a. Tuni rashin waɗannan kuɗaɗe ya shafi harkokin kasuwanci da kuma na yau da kullum a cikin ƙasar. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki Dr Isa Abdullahi. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana......
-
Dr. Abdulhakim Garba Funtua: Makomar Syria a ƙarƙashin sabuwar gwamnati
13/12/2024 Duración: 03minMajalisar Ɗinkin Duniya ta shiga sahun ɓangarorin da suka fara nuna goyon baya ga sabuwar gwamnatin Syria, a wani yanayi da shugaba Abu Mohammad al-Julani da Firaminista Mohammed al-Bashir suka faro shugabancin riƙon kwarya gadan-gadan, kodayake kiraye-kiraye na ci gaba da tsananta don ganin jagororin sun yi taka-tsan-tsan a salon mulkinsu don kaucewa sake faɗawar ƙasar a yaƙi. Dangane da wannan Azima Bashir Aminu ta tuntuɓi masanain alaƙar ƙasashen ƙetare Abdulhakeem Garba Funtua, don jin ko wannan gwamnati za ta samu cikakken goyon bayan yammacin duniya.Ku latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawarsu
-
Kwamared Nuhu Abayo Toro: Kan matatar mai ta Fatakwal
10/12/2024 Duración: 03minƘungiyar Kwadago ta Najeriya ta ziyarci matatar man fetur ta birnin Fatakwal bayan gwamnatin ƙasar ta ce matatar ta fara aiki gadan-gadan. Domin jin yadda wannan matata ta fara aiki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Kwamare Nuhu Abayo Toro, ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar kwadagon da suka ziyarci matatar.Ku lata alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
-
Irbaɗ Ibrahim: Yadda John Mahama ya lashe zaɓen Ghana
09/12/2024 Duración: 03minAn kammala zaɓen shugaban ƙasar Ghana, ba tare da fuskantar wata matsala ba, duk da cewa an yi hasashen za'a iya fuskantar tashin tashina a lokacin zaɓen. Sakamkon zaɓen na ƙarshen mako ya nuna cewa tsohon shugaban kasa John Mahama ne ya lashe saben, kuma tuni ɗan takaran jam’iyya mai mulki, Mahamudu Bawumia ya taya shi murya, abin da ke nuni da cewa ya amince da shan kaye.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar tattaunawar Bashir Ibrahim Idris tare da Alh. Irbaɗ Ibrahim, masanin siyasa a Ghana
-
Ambasada Abubakar Chika kan martanin da ake maidawa na kifar da gwamnatin Assad
09/12/2024 Duración: 03minƘasashen duniya sun fara mayar da martani dangane da nasarar da ƴan tawaye suka samu na karɓe iko da birnin Damascus tare da tserewar shugaba Bashar Al Assad. Yayin da wasu ke murna dangane da kawo ƙarshen Assad a karagar mulki, wasu kuma na bayyana damuwa akan makomar yankin Gabas ta Tsakiya. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Jakadan Najeriya a ƙasar Iran, Ambasada Abubakar Chika. Ku latsa alamar sauti domin jin yadda zantawarsu ta gudana........
-
Mun biya ƴan bindiga kafin mu yi noma amma sun hana mu girbi - mazauna Zamfara
05/12/2024 Duración: 03minMazauna yankunnan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya na ci gaba bayyana irin halin kuncin rayuwa da suka samu kansu sakamakon yadda suke biyan ƙudi ga ƴan bindiga kafin su yi noma a daminar da suka gabata, yanzu kuma lokacin girbi ƴan bindigar sun hana su zuwa girbi da kwaso amfanin gonar sai sun biya.Wannan matsala ta yi sanadiyar talauta akasarin mutanen da ke wannan yankin. Dangane da wannan batu ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, kuma ga abinda ya shaida masa.
-
Satar manyan jami'an gwmanati na ci wa 'Yan Najeriya tuwo a ƙwarya
04/12/2024 Duración: 03min'Yan Najeriya na ci gaba da bayyana bacin ransu danagane da satar da wani tsohon babban jam'in gwamnati ƙasar ya yi, ya kuma gina gidaje sama da 750. Tuni kotu ta ƙwace gidajen da kuma mallakawa gwamnati. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Bala Ibrahim mai sharhi kan lamuran yau da kullum, kuma ga yadda zantawar tasu ta gudana. Sai a latsa alamar sauti domin sauraron shirin.
-
Satar manyan jami'an gwamnati na ci wa 'yan Najeriya tuwo a ƙwarya
04/12/2024 Duración: 03minƳan Najeriya na ci gaba da bayyana ɓacin ransu dangane da satar da wani tsohon babban jami'in gwamnatin ƙasar ya yi, ya kuma gina gidaje sama da 750. Tuni kotu ta ƙwace gidajen da kuma mallakawa gwamnati, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Bala Ibrahim mai sharhi kan lamuran yau da kullum, kuma ga yadda zantarwarsu ta gudana.
-
Tattaunawa da Muhammad Dahiru Dan Adam kan ƙalubalen naƙasassu a jihar Lagos
03/12/2024 Duración: 03minYau ce ranar da Majalisar ɗinkin duniya ta ware domin tunawa da halin da masu buƙata ta musamman ke ciki da kuma duba hanyoyin da za a inganta rayuwarsu. Karibullahi Abdulhamid Namadobi ya yi tattaki zuwa wani gida a jihar Lagos mai ɗauke da irin waɗannan mutanen sama da dubu 3 da suka fito daga yankunan arewacin Najeriya. Ga yadda zantawarsa ta gudana da guda cikin shugabanninsu Muhammad Dahiru Dan Adam.
-
Nasir Kabir kan yajin aiki a wasu jihohin Najeriya kan mafi ƙarancin albashi
02/12/2024 Duración: 03minYau ma'aikan gwamnati a jihohi kusan 15 na Najeriya ke fara yajin aiki saboda ƙin biyansu mafi ƙarancin albashin naira dubu 70 da sabuwar doka ta tanada. Ƙungiyar kwadago ta ƙasar ta bai wa jihohin umarnin fara yajin aikin. Saboda haka Bashir Ibrahim Idris ya tintibi Sakataren tsare tsaren ta Comrade Nasir Kabir. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana........
-
Ngozi Okonjo Iweala ta sake zama shugabar WTO
29/11/2024 Duración: 03minHukumar Kasuwanci ta duniya WTO ta bai wa tsohuwar ministan kudin Najeriya Ngozi Okonjo Iweala wa'adi na 2 na shekaru 4, yayin da ta kawo karshen wa'adinta na farko. Wannan ya biyo bayan kasancewarta 'yar takara daya tilo da ta sake neman mukamin.Domin tasirin wannan nadi da kuma kalubalen dake gabanta, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dakta Isa Abdullahi, masanin tattalin arziki a Najeriya.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
Tattaunawa da Mele Kyari kan fara aiki a matatar mai ta Fatakwal da NNPCL ta sanar
27/11/2024 Duración: 03minA Najeriya bayan shafe shekaru da dama ana gyaran matatar man fetur na ƙasar da ke birnin Fatakwal a jihar Ribas, kamfanin man fetur na kasar NNPCL ya sanar da kammala gyarar a ranar Talata, inda ya kuma ce ba tare da wani bata lokaci ba tuni aka fara dakon man.NNPCL ya kuma shaida cewa sauran matatun mai na ƙasar, wato na Warri da Kaduna ma za su fara aiki ba tare da sanar da takamammen ranar da hakan zai kasance ba. Wakilinmu na Abuja, Mohammed Sani Abubakar ya tattaunawa da shugaban kamfanin na NNPCL Mele Kyari. Ku latsa alamar sauti domin jin hirar da aka yi da shi...
-
Dr. Kasum Kurfi kan rahotan NBS na farfadowar tattalin arzikin Najeriya
26/11/2024 Duración: 03minHukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS, ta ce tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kashi 3.46 a rubu'i na uku na wannan shekarar ta 2024, wato tsakanin watan Yuli zuwa Satumba. A rahoton da ta fitar ranar Litinin, NBS ta ce yawan masara aikin yi ma ya ragu a Najeriya. Kan haka ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki Dr Kasum Garba Kurfi.
-
Sanata Umar Ibrahim Tsauri kan matsayar gwamnonin PDP halin da Najeriya ke ciki
25/11/2024 Duración: 03minA ƙarshen makon da ya gabata ne gwamnonin PDP suka gudanar da taronsu a jihar Filato, wanda ya tattauna halin da Najeriya ke ciki da kuma makomar jam'iyyarsu. Bayan kammala taron gwamnonin sun buƙaci shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu da ya sake nazari kan manufofinsa na tattalin arziki saboda illar da yake yiwa talakawa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Sakataren Jam'iyyar PDP na ƙasa, Sanata Umar Ibrahim Tsauri. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar zantawarsu..........